<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Sunan Yesu Shi Ne Mafi Ɗaukaka LW289</title>
<lyrics>[V1]
 1) Sunan Yesu shi ne mafi ɗaukaka
 Cikin dukan sunaye.
 Babu wani suna wanda ya isa
 Cetonmu, sai shi kaɗai.

[V2]
 KORUS
 Yesu ne Mai Ceto,
 Ba wani Allah za mu bi,
 Cikin sunansa, nasara,
 Babu shakka, za mu yi.

[V3]
 2) Yesu ya ci nasara da zunubi,
 Ba da ikon duniya ba,
 Sai ta wurin mutuwa da tashinsa
 Daga cikin kabari.
 Korus

[V4]
 3) Halin Almasihu mu ke so mu yi,
 Ruhunsa ya cika mu
 Don mu shaida shi ga dukan mutane,
 Cewa ya yi cetonsu.
 Korus

[V5]
 4) Sai mu ƙanƙantad da kanmu, ƴanuwa,
 Kamar yadda shi ya yi.
 Mu yi nufinsa da farar zuciya,
 Har matuka za mu bi.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>289</hymn_number>
</song>